AFCON: Buhari ya jinjina wa Super Eagles

AFCON: Buhari ya jinjina wa Super Eagles

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa tawagar kwallon kafa ta kasar kan rawar da take takawa a gasar cin kofin kasashen Afirka da ake yi a Masar.

A ranar Laraba ne Super Eagles ta kai zagayen kusa da na karshe bayan da ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-1.

Kwallon da William Troost-Ekong ya zura ana dab da tashi ita ce ta bai wa Najeriya wannan damar.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya taya ‘yan Super Eagles murna, yana mai cewa ‘yan kasar sun kagu su ga tawagar ta lashe wasa biyu nan gaba domin kawo kofin gida Najeriya.

Samuel Chukwueze ne ya fara zura kwallo a ragar Bafana Bafana bayan da Alex Iwobi ya bugo masa kwallo.

Bongani Zungu ya ramawa Afirka ta Kudu – kwallon da da farko aka soke saboda zargin satar gida amma daga baya na’urar da ke tallafa wa lafari ta ce babu satar gida, abin da ya sa aka amshi kwallon.

Sai dai dan wasan baya na Udinese Troost-Ekong ya samu nasarar jefa kwallo a raga ana dab da kammala wasa, wacce kuma ita ce ta raba gardama.

Ya ci kwallon ne cikin sauki bayan da kwallon da Moses Simon ya bugo ta kufcewa golan Afirka ta Kudu Ronwen Williams.

Najeriya za ta kara da Ivory Coast ko Algeria a wasan kusa da na karshe da za a buga ranar Lahadi da misalin karfe (8.00) na dare a gogon Najeriya da Nijar.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: