Amurka za ta kare Poland daga barazanar Rasha

Amurka za ta kare Poland daga barazanar Rasha

Shugaba Trump ya amince da yarjejeniyar tura wasu karin dakarun Amurka 1000 zuwa Poland, domin karfafa tsaron kasar, sakamakon fargabar da ake nunawa kan barazanar da kasar ke fuskanta daga Rasha.

Yayin wata ganawa a fadar gwamnatin Amurkar, White House, tsakanin Mista Trump da takwaransa na Poland Andrzej Duda, Trump ya ce Polanda da kanta za ta samar da sansani da kayayyaki domin zaman sojin.

Tun a shekarar da ta gabata gwamnatin Poland ta yi tayin bayar da dala biliyan biyu domin taimaka wa wajen samar da sansanin soji na dindindin a cikin kasarta, sansanin da Shugaba Duda ya kira da suna Fort Trump.

Yanzu wadannan karin soji da za a girke a wurare daban-daban a cikin Poland, ba za su kasance na dindindin ba, za su rika karba-karba ne akai akai domin taimaka wa sojojin Amurka 4500, wadanda tuni suke Poland din.

Shugaba Duda da yaba da wannan yarjejeniya a matsayin wata gagarumar nasara, duk da cewa abin da Poland din ta samu ya ragu matuka, kan wanda ta yi fata.

Gwamnatin kasar ta Poland a sonta ta so a ce an girke wani rukuni na sojojin Amurka masu manyan motocin yaki, sama da kashi 10 na abin da aka yi mata alkawari, wadanda kuma za a zaunar da su dindindin a a sansanin.

Duk da hakan Shugaba Duda ya ce yana fatan a hankali a hankali za a rika kara yawan dakarun na Amurka.

Ita dai Poland kamar sauran kasashe da ke bangaren gabas na kungiyar tsaro ta NATO, tana cike da fargaba cewa za ta iya kasancewa kasa ta gaba a mamaya ko harin Rasha, bayan wanda Moscow ta yi wa Georgia da Ukraine.

Babban Sakataren kungiyar NATON Jens Stoltenberg, ya yi maraba da sanarwar, yana mai cewa ta nuna gagarumin kudurin Amurka na tabbatar da tsaron Turai.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: