An ceto ‘yan Turkiyya da aka sace a jihar Kwara

An ceto ‘yan Turkiyya da aka sace a jihar Kwara

‘Yar Turkiyyan nan guda hudu da masu garkuwa suka sace a jihar Kwara a makon da ya gabata sun samu ‘yanci daga masu garkuwa da su, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar ta Kwara ta tabbatar..

‘Yan bindiga ne dai suka yi awon gaba da ma’aikatan su hudu a wata mashaya.

Masu garkuwar sun nemi da a ba su kudin fansa dala miliyan daya amma ‘yan sanda sun ce an kubatar da wadanda aka yi garkuwar ba tare da biyan kudi ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kwara, Kayode Egbetokun ya ce an samu ‘yar turkiyyar su hudu a yashe a wani daji ranar Juma’a.

‘Yan sandan rundunar jihar ne suka kaddamar da neman Turkawan bisa hadin gwiwar ‘yan sintiri da kuma tawagar ‘yan sanda daga birnin Abuja.

Mr Egbetoku ya ce kama wasu masu garkuwa da jama’a guda uku ne ya taimaka wajen gano Turkawan.

Tuni dai aka duba lafiyar mutanen hudu bayan sakin su.

Jakadan Turkiyya a Najeriya, Melih Ulueren ya ce ya yi farin ciki dangane da ceto ‘yan kasar tasa.

Garkuwa da mutane dai ya zama ruwan dare, inda masu satar mutanen ke harar baki ‘yan kasashen waje da ‘yan Najeriyar masu idanu da tozali.

Ko a makonni biyun da suka gabata sai da aka yi barayin jirgin ruwa suka kai wa wani jirgin ruwa mallakar kasar Turkiyya hari inda suka yi garkuwa da matuka jirgin Turkawan 10. Har yanzu ba amo babu labari.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: