An gurfanar da gimbiyar Saudiyya gaban shari’a

An gurfanar da gimbiyar Saudiyya gaban shari’a

Gimbiyar masarautar Saudiyya da ake zargi da bai wa mai tsaron lafiyarta umarnin cin zarafin wani ma’aikaci na fuskantar shari’a a birnin Paris, sai dai ba ta bayyana gaban kotun ba.

Hassa bint Salman kanwa ce ga yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, cikin tuhume-tuhumen da ake mata har da amfani da makami da hadin baki wajen garkuwa da mutane.

Shi ma mai tsaron lafiyarta da akai zargin ya tilastawa ma’aikacin sunbatar kasan kafarta a lokacin da lamarin ya faru a shekarar 2016 an gurfanar da shi gaban kuliya.

Gimbiya Hassa wadda aka bada sammacin kamata da mai tsaron lafiyarta sun musanta zargin da a kai musu.

Harwayau dukkan mutanen biyu wato Gimbiya Hassa da wanda ya yi kararta Ashraf Eid ba su halarci zaman kotun ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

To amma a zaman da aka yi na kotun a ranar Talata mai tsaron lafiyarta Rani Sa’idi ya halarta kewaye da ‘yan uwansa.

Lauyan da ke kare gimbiya Hassa, Emmanuel Moyne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zargin da ake yi ma ta bita-da-kulli ne kawai.

”Gimbiya Hassa mace ce mai karamci, da kyautatawa, tana da sanyin hali”, in ji Mista Emmanuel.

Wadanne zarge-zarge ake ma ta?

A watan Satumbar 2016 ne, wani ma’aikaci dan asalin kasar Masar Ashraf Eid, ya shaida wa ‘yan sanda cewa lokacin da ya fara aiki a gidan masarautar Saudiyya da ke rukunin gidajen masu hannu da shuni da ke Avenue Foch a birnin Paris ya shiga bandaki tare da daukar hoton yadda tsarinsa ya ke a ranarsa ta farko da kama aiki saboda halin mantuwa ta hanyar amfani da wayarsa ta salula.

Kwatsam sai gimbiya Hassa ta yi zargin ya na son sayar da hotonta da ya dauka ta na tsaye a gaban madubin bandakin, don haka ta kira mai tsaron lafiyarta saboda dokokin kasar Saudiyya sun haramta daukar hoton gimbiyar.

Kamar yadda ‘yan sandan Faransa suka rawaito, ma’aikaci Ashraf ya zargi gimbiyar da shaida wa mai tsaron lafiyarta cewa ”Ya zama dole a kashe wannan karen, bai kamata ya ci gaba da rayuwa ba. Za ka ga yadda ake magana da gimbiya ko ‘ya’yan masarautarmu.”

Ashraf ya ce daga nan ne mai tsaron lafiyarta ya lakada masa duka tare da tilasta shi ya sumbaci karkashin kafarta.

Amma mai tsron na ta ya ce ya ji gimbiyar tana ihun a kawo mata dauki, don haka sai ya garzaya da gudu anan ya tadda suna jani-in-jaka tsakaninta da ma’aikacin don karbe wayar salular.

”Dan haka sai na kama shi da karfi, tare da rike hannayensa saboda ban san abin da yake son aiwatarwa ba”, in ji Mista Rani tare da musanta zargin cin zarafin ma’aikacin.

Bayan sa’o’i masu yawa ne aka saki ma’aikacin tare da fasa wayar salularsa.

Lauyoyin da ke kare gimbiyar da mai tsaron lafiyarta sun yi watsi da zarge-zargen tare da cewa kwanaki kadan bayan afkuwar lamarin ma’aikaci Asharaf ya kawo wata takarda da ya bukaci a biya shi kudi dala 23,500, kusan naira miliyan 10.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: