An koma wani zagayen tattaunawa a Sudan

An koma wani zagayen tattaunawa a Sudan

Bayan afka wa masu zanga zangar neman kafuwar mulkin farar hula da yayi sanadiyyar rayuka a Sudan, an bude sabon zagayen tattaunawa da majalisar mulkin sojin kasar.

A jiya Talatar ne aka sake komawa kan teburin tattaunawa tsakanin jagororin mulkin Sojin kasar Sudan da na bangaren masu zanga-zangar, domin ganin an maida mulki hannun farar hula, biyo-bayan barkewar wani sabon rikici a daren Litinin da ya yi sanadiyyar hallaka mutum shida ciki har da jami’in tsaro guda. 

Masu zanga-zangar dai sun taka gagarumar rawar da ta kawo karshen mulkin kama-karya na shekaru 30 na Al-Bashir, sai dai bayan sojoji sun hambarar da shi sai suka zama ‘yan kama-wuri-zauna, lamarin da ya fusata matasan sake fantsama kan titunan kasar suna kiraye-kirayen mika mulkin hannun farar hula.

Amurka dai ta zargi rundunar Sojin kasar da hannu wajen harin na jiya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida. DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: