An sallamo tsohon shugaban Kenya Daniel Arap Moi daga asibiti

An sallamo tsohon shugaban Kenya Daniel Arap Moi daga asibiti

An sallami tsohon shugaban Kenya Daniel Arap Moi daga asibiti bayan ya shafe kwanan 10 yana jinya.

Wani kakakin shugaban kasar ne ya shaida wa BBC wannan lamarin, amma bai bayyana irin rashin lafiyar da ya ke fama da ita ba.

Kakakin ya sanar da cewa tsohon shugaban mai shekara 95 a halin yanzu yana gidansa inda ya ke murmurewa.

Mista Moi shi ne yafi kowa dadewa kan karagar mulki a Kenya, bayan da ya shafe shekara 24

daga 1978 zuwa 2002 yana mulki.

Ya mulki kasar da karfin ikon da mulki ya ba shi, kuma an sha tuhumarsa da taka hakkin al’umomin kasar.

Amma bayan da ya fuskanci matsanancin matsin lamaba, sai ya amince da kafa jam’iyyu masu dama a 1992 a kasar.

A farkon wannan shekarar ne wata kotu ta umarci Mista Moi ya biya wata mata shiulling biliyan 1.06 (wato dala miliyan 10.5) saboda ya kwace mata wani filinta ba tare da hujja ba.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: