An soke ‘yan aikin tsaro na sa-kai a wasu jihohin Arewa

An soke ‘yan aikin tsaro na sa-kai a wasu jihohin Arewa

Gwamnonin jihohin arewa maso yamma da na arewa ta tsakiyar Najeriya sun yanke shawarar haramta ayyukan masu aikin sa-kai na tabbatar da tsaro (‘yan kwamiti) a daukacin jihohinsu.

Matakin yana daya ne daga cikin matsayar da suka cimma a wani taro, da aka yi a Katsina, na samo hanyoyin warware matsalar tsaro wadda ta addabi jihohin yankunan na Arewa, a jiya Alhamis.

A lokacin taron an gayyaci masu ruwa da tsaki a harkar, wadanda suka hada da babban sufeton ‘yan sandan kasar, Mohammed Abubakar Adamu da kuma wakilan Fulani na jihohin da matsalar tsaron ta fi kamari.

A wata tattaunawa da namema labarai, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce, yanzu sun “haramta duk wani mai aikin sa-kai na tsaro, wadanda daga sun ga wani Bafulatani sai su kashe shi”.

Kuma ya ce duk wanda aka samu ya aikata wani abu na “ta’addanci a irin wadannan ‘yan sa-kai” da aka rushe a yanzu za a kama shi kuma a hukunta shi.

Gwamna Masari ya ce sun yanke shawarar ne saboda ba sa yin aikin yadda ya kamata, musamman ma da a yanzu rundunar ‘yan sanda za ta fito da ka’idojin yadda za a kafa kwamitin aikin hadin gwiwa na ‘yan sanda da al’umma a unguwanni.

“Wannan shi ne zai fi amfani kasancewa zai zama kan doka da oda,” a cewar gwamnan, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin yankin arewa maso yamma.

Ganin cewa ba a kai ga samar da tsarin hadin gwiwar na ‘yan sanda da al’ummar unguwanni ba, aka soke ‘yan sa-kan, Alhaji Masari, ya ce, a wurin taron “Fulani sun yi alkawari cewa daga ranar Alhamis din nan ba za su sake kai farmaki ba kan garuruwa, suna satar mutane ko dabbobi ba”.

Sannan su ma Fulanin an ba su tabbacin cewa daga yanzu, “su da matansu za su iya zuwa kasuwanni matsawar ba su je da makamai ba, kuma za a bukace su, su mayar da dabbobin jama’a da suka sace, sannan su mika makaman da ke hannunsu”.

A nasu bangaren gwamnonin sun ce za su dauki matakin kyautata rayuwar Fulanin da dabbobinsu, ta hanyar gyara madatsun ruwa, da samar da makarantu na addini da na boko, da raya wuraren kiwo, in ji gwamnan jihar ta katsina.

Sannan kuma ya ce, za su bukaci gwamnatin tarayyar Najeriyar ta bayar da gudummawa domin tallafa wa Fulanin kamar yadda ake taimaka wa wadanda wata annoba ta fada musu.

A jihohi da dama na arewacin Najeriya, musamman Zamfara da Katsina, ‘yan bindiga sun hallaka jama’a da dama tare da sace wasu domin karbar kudin fansa da sace dabbobi da kona garuruwa. BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: