An yanke wa madugun adawa a Benin hukunci

An yanke wa madugun adawa a Benin hukunci

Wata kotun kasar Benin ta yanke wa madugun adawar kasar hukuncin daurin talala na watanni shida saboda karya dokokin zabe da ta ce ya yi.

Majiyoyi a kotun sun kuma ce an haramta wa dan adawar wato Lionel Zinsou, wanda tsohon Firaminista ne a kasar tsayawa takara na tsawon shekaru biyar.

An dai sami dan siyasar ta Benin ne da laifin mika takardun boge da kuma kashe kudi fiye da kima lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a shekarar 2016.

Wannan hukuncin na daga cikin tarnaki na baya-bayan nan da bangaren adawa ke gani karkashin shugabancin Shugaba Patrice Talon wanda ake zargi da muzguna wa ‘yan hamayya.

Tsohon shugaban Benin Boni Yayi ma dai ya sulale ne daga kasar cikin watan Yunin da ya gabata da sunan neman lafiya a ketare, bayan daurin na talala da shi ma aka yi masa saboda sukar tsarin da ake gudanar da majalisa a kasar. DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: