Bakin haure sun salwanta a teku

Bakin haure sun salwanta a teku

Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure daga kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara ya kife a tekun Bahar Rum, inda ake fargabar asarar rayuka.

Sama da mutum 70 ne ke a jirgin na ruwa, inda aka tabbatar da mutuwar uku sauran kuwa suka bace a cewar jami’an kasar Tunisiya da lamarin ya faru.

Ma’aikatar tsaron kasar ta Tunisiya ta ce ana can ana amfanin da dabaru daban-daban, na ganin an tsamo gwamman mutanen da suka nitse a ranar Juma’a.

Tekun Bahar Rum dai ya kasance wane wajen da ke lakume rayukan jama’a galibinsu Afirkawa, wadanda ke hankororn ketarawa kasashen Turai, ala kulli halin. DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: