Barcelona ta sayi matashin dan wasan Ingila

Barcelona ta sayi matashin dan wasan Ingila

Barcelona ta sayi dan wasan tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 16 Louie Barry kan kwantiragin shekara uku daga West Bromwich Albion.

Barry ya kasance a West Brom tun yana dan shekara shida amma ya ki amincewa ya bugawa babbar kungiyar kulob din.

West Brom za su samu fam 235,000 a matsayin lada daga Barcelona, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Barcelona ta ce Barry zai buga wa tawagarta ta ‘yan kasa da shekara 19 a kaka mai zuwa.

Akwai bukatar West Brom da hukumar kwallon kafa ta FA su amince da cinikin kafin ya tabbata, amma ana ganin hakan ba matsala ba ne.

Barca ta ce Barry na daga cikin kwararrun matasan ‘yan kwallo a Ingila.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: