Bincike ya gano shan kayan zaki na janyo ‘cutar daji’

Bincike ya gano shan kayan zaki na janyo ‘cutar daji’

Ababen sha masu zaki ciki har da ruwan ‘ya’yan itatuwa – na iya kara yiwuwar kamuwa da cutar daji, a cewar wasu masana kimiyya ‘na kasar Faransa.

An gano alakar cutar da shan ababen zakin ne bayan da aka gudanar da wani bincike da aka wallafa a mujallar British Medical Journal, wanda kuma ya duba sama da mutane 100,000 a cikin shekaru biyar.

Tawagar masanan ta Jami’ar Sorbonne Paris Cite ta nuna cewa tasirin da sikari ke yi a cikin jini na iya zama dalilin alakar.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da sahihancin binciken ba kuma masana sun yi kira da a sake dubawa.

Wadanne ne ababen sha masu zaki?

Masanan sun bayyana su a matsayin lemukan da yawan sikarin da ke cikinsu ya wuce kashi biyar cikin dari.

Ciki har da ruwan ‘ya’yan itatuwa (ko ba a kara masu sikari ba), lemukan kwalba da madarar da aka kara wa sikari da lemukan kara kuzari da shayi da kofi da aka kara wa sikari.

Tawagar masanan sun kuma duba ababen sha marasa zaki kuma sun gano cewa ba su da alaka da cutar dajin.

Ya ya girman hadarin kamuwa da cutar dajin yake?

Binciken ya gano cewa shan ababe masu zaki da yawansu ya kai mili lita 100 a rana na kara yiwuwar kamuwa da cutar daji da kashi 18%.

Cikin mutane 1,000, mutum 22 sun kamu da cutar dajin.

“Don haka wannan na nuna cewa akwai sahihiyar alaka tsakanin shan ababen sha masu zaki da kamuwa da cutar daji kuma hakan na bukatar karin bincike,” in ji Dakta Graham Wheeler, babban mai bincike a Asusun Binciken cutar Daji na Burtaniya.

Cikin nau’o’in cutar daji 2,193 da aka gano a yayin binciken, guda 693 sankarar mama ce, guda 291 cutar dajin mafitsara ce sannan guda 166 na ciki ne da dubura.

Kiba na daya daga cikin manyan abubuwan da ke janyo cutar daji, kuma yawan shan ababen sha masu zaki na janyo kiba.

Sai dai binciken ya ce ba a nan gizo ke saka ba.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: