Dalilin Hana Duk Wani Nau’in Gangami a Kano – ‘Yan sanda

Dalilin Hana Duk Wani Nau’in Gangami a Kano – ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta kare kanta kan dalilin da ya sa ta dauki matakin haramta duk wani nau’in taro a daukacin jihar, inda ta ce matakin na da nasaba da kokarin ganin an tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Rahotanni da dama sun ruwaito kakakin rundunar jihar DSP Abdullahi Haruna a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar a yau Asabar kan dalilin daukan wannan mataki.

A cewar rundunar ‘yan sandan, daukan matakin ya zama dole domin a kawar da duk wata barazana, ko daukan doka a hannu lura da irin barazanar da jihar fuskanta a ‘yan kwanakin nan.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta Kano, tayi  gargadin cewa, duk wanda ya saba wannan doka, zai fuskanci fushin hukuma kuma za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Masu lura da al’umara, sun yi sharhin cewa, wannan mataki bai rasa nasaba da rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da masarautar jihar.

Hukumar yaki da rashawa a jihar ta Kano tana tuhumar Sarki Muhammadu Sanusi II da ya yi bayani kan wasu kudade sama da biliyan uku da ake zargin an yi almubazzarancinsu wajen tafiyar da harkokin masarautar.

VOA

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: