Dan takarar jam’iyyar PDP a 2019 ya ce damar da yake da ita kan zabe ta kare

Dan takarar jam’iyyar PDP a 2019 ya ce damar da yake da ita kan zabe ta kare

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 na jam’iyyar adawa ta PDP, Ahaji Atiku Abubakar ya amsa cewa damar da yake da ita, domin bin kadin zabe a gaban kotu, ta riga ta kare.

Ya ce hukuncin, wani bangare ne na kalubalen dimokradiyya, wanda ya zama dole su tunkara a matsayinsu na kasa.

Jagoran adawar na wannan bayani a matsayin martani bayan hukuncin Kotun Kolin kasar wadda ta yi watsi da karar da ya daukaka.

Alkalan Kotun Kolin dai sun yi watsi da daukaka karar bisa dalilan rashin makama, inda kuma suka ce nan gaba za su bayar da dalilan da suka dogara da su.

Dan takarar na PDP ya yi wannan jawabi a shafinsa na twitter bayan hukuncin kotun kolin na ranar Laraba.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce hanyar shari’a da ya dauka duk da cewa ta zo karshe, a saboda haka duk wata dama da yake da ita ta kare.

Alhaji Atiku ya kuma ce an yi adalci a hukuncin ko ba a yi ba alkalanci ya rage wa ‘yan Najeriya inda ya ce a amatsayinsa na wanda ya yi imani da tsarin demokradiyya ya yi fafutuka domin al’ummar Najeriya, kuma zai ci gaba da wannan fafutuka domin tabbatar da dorewar dimokradiyya da wanzuwar adalci,

Ya kara da cewa a tsarin dimokradiyya ana bukatar bangaren shari’a mai karfi da sakar wa ‘yan jaridu mara da kuma barin hukumar zabe ta yi aiki ba tare da fiifta wani bangare ba.

Sai dai Atiku ya ce a Najeriya babu ko daya daga cikin wadannan abubuwa da ya zayyana a yanzu haka.

Dan takarar na jam’iyyar PDP ya ce ya kamata nasarar dimokradiyya ta kasance ‘mutum daya kuri’a daya’ amma idan aka yi watsi da hakan to fa an kama hanyar balbalcewa.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: