Divock Origi zai ci gaba da zama a Liverpool

Divock Origi zai ci gaba da zama a Liverpool

Dan wasan gaba na Liverpool Divock Origi ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya bayan taimakawa kulob din lashe gasar Zakarun Tiurai.

Dan kwallon na Belgium mai shekara 24, ya koma Liverpool ne daga Lille a 2014 amma ya shafe shekara biyu a matsayin aro a wajen Anfield.

Sai dai ya taka rawar gani bayan ya dawo a bara, inda ya zura kwallo biyu a wasansu da Barcelona sannan ya ci kwallo ta biyu a wasan karshe su da Tottenham.

“Na dade ina jin cewa ina so na ci gaba da zama a nan,” a cewar Origi. “Akwai wani abu na musamman tattare da zama a nan.”

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: