Ebola na neman raba Ruwanda da Kwango

Ebola na neman raba Ruwanda da Kwango

Ministar kiwon lafiyan kasar Ruwanda ta musanta cewar sun rufe kan iyakarsu da Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango a bisa yaduwar cutar Ebola.  Diane Gashumba  ta ce kan iyakar ba wanda ya rufe ta. Ministar kiwon lafiyan ta yi jawabin ne tana tsaye a gefen ministan harkokin waje Olivier Nduhungirehe wanda tun da farko shi ne ya fada wa manema labarai cewa Ruwanda ta rufe kan iyakarsu da Kwango bisa bullar cutar Ebola yankin Goma, wannan labarin dai ya harzuka gwamnatin Kwango. Wadannan jawabai masu karo da juna da ke fitowa daga kasar Ruwanda, sun biyo bayan samun mutane hudu dauke da cutar Ebola a yankin Goma. Goma mai yawan mutane miliyan biyu, yana da matukar alaka da kasar Ruwanda, inda ake samun zirga-zirgar motoci.  DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: