Guardiola na iya komawa Serie A, Ibrahimović zai koma AC Milan

Guardiola na iya komawa Serie A, Ibrahimović zai koma AC Milan

Dan wasan tsakiya na Arsenal Granit Xhak zai iya barin kulob din a watan Janairu kuma a shirye Newcastle United take ta sayi matashin mai shekara 27 dan kasar Switzerland. (Times – subscription required)

Barcelona ta nuna sha’awarta ta sayen dan wasan gaba na kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang mai shekara 30 daga Arsenal, kuma za ta iya yin hakan a watan Janairu. (El Chiringuito via Mirror)

Dan wasan tsakiya na Uruguay Lucas Torreira mai shekara 23 ya shirya tsaf don tattauna wa a mako mai zuwa kan makomarsa a Arsenal. (Mirror)

A shirye Zlatan Ibrahimović yake don koma wa AC Milan bayan da dan wasan mai shekara 38 ya bar kungiyar LA Galaxy. (ESPN, via Calciomercato)

Dan wasan gaba na kasar Norway Erling Braut Haaland mai shekara 19 zai iya kin karbar tayin komawa kungiyoyi irin su Manchester United da Liverpool da Arsenal, ya koma kungiyar RB Leipzig ta Bundesliga daga kungiyarsa ta Red Bull Salzburg a bazarar badi. (Sky Sports)

A shirye kocin Manchester City Pep Guardiola yake ya koma horarwa Italiya, idan kwantiraginsa ta kare a Premier a karshen kakar badi. (Times – subscription required)

Dan wasan Burnley da kuma tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21 Dwight McNeil mai shekara 19, ya ce ya fi mayar da hankali a kan kwallonsa maimakon biye wa jita-jitar da ake yadawa ta alakanta shi da kungiyar Manchester United. (Mirror)

Manchester United da Tottenham da Wolves suna gasa kan batun daukar dan wasan gaba na Colombian James Rodriguez mai shekara 28 daga Real Madrid a watan Janairu. (El Desmarque – in Spanish)

Kungiyar Crystal Palace na sa ido kan nasarar da dan wasan gaba na Netherlands Wout Weghorst mai shekara 27 ke samu, wanda ya ci kwallo takwas cikin wasa 15 da ya buga wa Wolfsburg zuwa yanzu a wannan kakar. (Calciomercato – in Italian)

Arsenal da West Ham suna gasa wajen kokarin sayen dan wasan gaba na Austria Martin Hinteregger mai shekara 27, kan kudi fam miliyan 22 daga Eintracht Frankfurt. (Sun)

Bournemouth da Wolves na sha’awar sayen dan wasan gaba na Ingila mai shekara 22 Karlan Grant daga Huddersfield a watan Janairu. (Sun)

Bayern Munich ba za ta dauki Arsene Wenger a matsayin kocinta ba duk kuwa da cewa tsohon kocin Arsenal din ya nuna sha’awar hakan lokacin da ya yi magana da mamallakin kulob din Karl-Heinz Rummenigge a wayar tarho. (Sky Sports)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers ya ce bai kamata tsoron fafatawa ta sa dan wasan gaba na Ingila Jamie Vardy mai shekara 32 ya ki koma wa Arsenal ba a lokacin da kungiyar ta so daukarsa a shekarar 2016. (Telegraph)

Dan wasan baya na Southampton Cedric Soares ya ce zai bar kungiyar a karshen kakar amma dai matshin dan kasar Portugal mai shekara 28 na son fara ceto kungiyar tukunna. (Telegraph)

Wani tsohon dan wasan Manchester United da Juventus ya ce zai iya sanya cacar pizza (wani abinci na Turawa) kan cewa dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba mai shekara 26, zai koma Italian Seria A.(Tuttosport, via Goal)

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: