Hassan Rouhani: Birtaniya matsoraciya ce

Hassan Rouhani: Birtaniya matsoraciya ce

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya kira Birtaniya da matsoraciya saboda amfani da jiragen sojin ruwa domin raka jirgin dakon mai zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Rouhani ya kuma gargadi Birtaniya ta kuka-da-kanta kan abin da zai biyo baya sakamakon kwace jirgin ruwan dakon man kasar da ta yi a makon da ya wuce.

Tuni tankar dakon man Birtaniya ta tsallaka gabar tekun Fujairah, bayan ta wuce ta mashigar Hormuz ba kuma tare da samun wata matsala ba.

An dai yi wannan tafiya ne da taimakon jirgin sojin ruwa na Birtaniyar, da alama kuma wannan mataki na daukar ‘yan rakiya ya fusata kasar Iran.

An ambato Shugaba Rouhani cikin kakkausan lafazi tamkar yadda wanda ya gada Mahmoud Ahmadinajad ke yi, yana cewa Birtaniya ta zama farar kura wajen tsoro.

Har yanzu Iran na jin haushin kwace tankar man ta da aka yi wadda ke kan hanyar zuwa Siriya.

Birtaniya ta ce an dauki matakin ne saboda dakon man ya sabawa takunkumin da Tarayyar Turai ta kakaba wa Siriyar.

Haka kuma, Iran din na zargin kasashen Birtaniya da Jamus da Faransa da kin daukar matakin sassauta takunkuman da Shugaba Trump na Amurka ya sake kakaba ma ta tun bayan ficewarsa daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

A bangare guda hukumar da ke sa ido kan kera makaman nukiliya ta yi gargadi kasashen da ke cikin yarjejeniyar su ja wa Iran kunne tare da shan alwashin daukar mataki matukar ta ci gaba da samar da makamashin Uranium.

A irin sakonnin da ya ke wallafawa a shafinsa na Twitter, Shugaba Donald Trump ya yi barazanar sake kakaba wasu takunkuman ga Iran.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: