Holland ta haramta burqa da nikabi

Holland ta haramta burqa da nikabi

Kasar Holand ta fara aiki da dokar haramta duk wani abu da zai rufe fuskar mutum kamar burqa da nikabi a bainar jama’a, tare da cin tarar kudi ga duk wanda ya karya dokar.

Daga cikin wuraren da dokar za tayi  aika sun hada da gine-ginen gwamnati da asibitoci da makarantu da motoci da jiragen haya da ke jigila a sassan kasar.

Tuni dai kungiyoyin Musulmi da na kare hakkin dan Adam a kasar suka nuna rashin amincewarsu da dokar yayin da wata jam’iya da ke da alaka da addinin Islama a birnin Rotterdam ta ce za ta biya tarar Euro 150 da za a karba ga duk wanda hukuma ta kama da karya dokar. 

Wani dan majalisa mai suna Geert Wilders da ya yi fice wajen sukar addinin Islama a kasar ne ya fara tado da maganar haramta amfani da Burka a kasar shekaru 10 da suka gabata kafin daga bisani majalisar dokokin kasar ta amince da batun a shekarar da ta gabata.

DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: