Ihya’us Sunnah

Shi dai shirin Ihya’us Sunnah shiri ne na addinin musulinci, wanda ake gabatarwa da karfe 6:30 am, na safiyar kowace rana, ba a maimaitawa. Mallam Saminu Abdulkadir Yakasai ne ke fassara littafin na Ihya’ussunnah wa’ikmadul bid’a, wanda Shehu Usman Dan Fodiyo ya rubuta. Kuma littafin ya kunshi babi 33 kan hukuncin rayuwa a addinin musulinci, sannan littafin ya fi ba da karfi kan riko da sunnar Annabi Muhammadu S.A.W da sahabbansa da tabi’ai da tabi’ittabi’ina.