Iya Ruwa, Fidda Kai

Iya Ruwa, Fidda Kai shiri ne na Siyasa tsawon mintina 25 a ranakun litinin zuwa Juma’a daga karfe 8:30 zuwa 8:55 na dare, a tagwayen tashoshinmu na AM/FM,Radio Kano. Ana maimaita shirin washegari da karfe 8:00 zuwa 8:25 na safe a iya tashar AM kawai.
Shirin yana tattaunawa da ‘Yan Siyasa manya da kanana a fagen al’amurran siyasar kasarnan da ma na wasu sassan Duniya.
Kazalika shirin kan tattauna da masharhanta da manazarta harkokin Siyasa da Tattalin arziki.
Babbar manufar shirin Ita ce wayar da kan Al’ummar kasa game da hanyoyin bi wajen bunkasa ci gaban kasa a karkashin mulki irin na Siyasa.