Jakadan Burtaniya a Amurka ya yi murabus

Jakadan Burtaniya a Amurka ya yi murabus

Sir Kim Darroch ya yi murabus daga matsayin jakadan Burtaniya a Amurka a dai-dai lokacin da ake tsaka da kace-nace kan kwarmata jerin imel-emel din da ya yi inda ya soki tsarin gwamnatin Shugaba Trump na Amurka.

Mista Trump dai ya bayyana jakadan na Burtaniya da ‘shashan mutum, bayan da imel din da jakadan ya rubuta inda ya kira Trump din da ‘dan bankaura wanda bai san makamar aiki ba.’

Ma’aikatar kasashen waje ta Burtaniya ta ce kwarmata bayanan ‘keta’ ce kuma Sir Kim ‘ya yi rawar gani.’

Sir Kim ya ce yana son kawo karshen cece-kuce , inda ya kara da cewa “ba abu ne mai yiwuwa ba” ya ci gaba da aiki ba tun da aka kwarmata bayanan da ke cikin imel din da ya rubuta.

A wata takarda da ya rubuta wa ma’aikatar harkokin waje cewa “Tun da aka kwarmata abubuwan da na rubuta a imel ake ta shaci-fadi kan mukamina da kuma sauran kwanakin da suka rage min na aiki.”

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: