Kadaura (Babbar Inuwa)

Shirine da gidan Redio kano yake gabatarwa kai tsaye (live) ta tagwayen tashoshinmu na AM da FM. A duk ranar Asabar da daddare, daga karfe 9.00 – 10.00 na dare tare da jami’in shirin. Nuhu Gudaji.
Manufar shirin shine don ya bayyanawa al’umar jihar kano irin ayyukan alherin da Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin maigirma Gwamnan jihar kano. Dr. Abdullahi umar Ganduje ofr. Khadimul islam take aiwatarwa don cigaban al’umar jihar kano tare da bawa masu sauraro damar bugo waya kai tsaye ga manyan jami’an Gwamnati don yin tambayoyi da karin bayani kan ayyukan Gwamnati wadanda basu fahimta ba tare da bada shawarwari kan irin muhimman bukatun al’umma ga Gwamnati.
Domin cimma manufar wannan shiri ,
muna Gayyato yan majalisar zartarwa na jiha wato kwamishinoni don su yi bayani da kansu kan irin makudan kudin da Gwamnati take kashewa ta karkashin ofishinsu don gudanar da aiyukan more rayuwa da cigaban al’umar jihar kano. Haka kuma a wasu lokutan mukan gayyato shugabannin kananan ma’aikatu wadanda wasu rassane na manyan ma’aikatun (ministries) kamar MD’s don suma suyi bayanin irin cigaban da aka samu a ma aikatunsu ta fagen aiyukan cigaban al’umma.