Kasashe na toshe Intanet don hana satar jarabawa

Kasashe na toshe Intanet don hana satar jarabawa

Satar jarabawa ta zama ruwan dare a lungu da sako a fadin duniya kuma kasashe na daukar matakai don dakile hakan ciki har da toshe layukan sadarwa.

Hukumomi a Najeriya sun dade suna kokawa kan yadda dalibai ke satar jarabawa musamman wadanda ake yi a kasa baki daya kamar JAMB da WAEC da NECO.

Kasar Habasha wato Ethiopia ta dauki matakin katse layin Intanet da ma na sakon tes a daidai lokacin da dalibai ke kokarin fara rubuta jarrabawa a fadin kasar, wanda wasu ke hasashen cewa an yi hakan ne don a dakile satar amsa.

Katsewar Intanet a kasar ta zama jiki yayin da kasar ta shiga kwana na uku ba tare da layin Intanet ba.

A ranar Laraba gidan talabijin din kasar ETV ya ruwaito cewa an kama wasu dalibai uku da satar amsa bayan sun turawa junansu sakon tes.

Kasar Aljeriya ma ta dauki irin wannan mataki na toshe kafar Intanet yayin jarabawar kasa baki daya.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito, a shekarar 2016 dalibai sama da 700,000 ne suka rubuta jarabawar fita daga sakandare wadda ake kira bac.

Ma’aikatar ilimin kasar ta soke dubbai daga cikinsu kuma ta tilasta sake rubuta wasu 500,000 ta hanyar sauya tambayoyin.

Daga bisani hukumomi sun kama mutum 31 ciki har da ma’aikatan hukumar ilimi da ake zargi da aikata laifin.

Baya ga wannan dambarwar, hukumar ilimin a shekarar 2017 ta kafa na’urorin katse layin salula a dakunan jarabawa 2,100 a fadin kasar kuma ta toshe Facebook da Twitter da Instagram.

Kasashe kamar Syria da Iraq da Mauritania da Uzbekistan duk sun bi sahu wajen toshe kafar Intanet ko kuma shafukan sada zumunta.

Malam Mahmud Sulaiman malami ne a makarantar sakandare ta GGISS Zaura Danbaba a jihar Kano kuma ya ce Intanet ce kawai madogarar dalibai.

Ya kara da cewa: “Daliban yanzu babu ruwansu da karanta littafi, idan jarabawa ta zo sai su shiga Intanet su karanta abubuwa su shiga dakin jarabawa.

“Akwai shafuka na musamman da aka bude wadanda aikinsu kawai shi ne su rubuta amsoshi, inda dalibai ke bayar da kudi ko katin waya kafin su samu.

“Idan aka toshe tabbas satar amsa za ta ragu, domin kuwa wajibi ne su karanta litattafansu”.

Mahmud ya ce sun sha kwace wayoyin salula daga hannun dalibai a dakin jarabawar.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: