Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe manoma 13

Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe manoma 13

‘Yan bindiga sun halaka mutane 13 a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. An kai harin ne a lokacin da manoma suka bazama gonakinsu bayan samun saukar ruwan sama a safiyar jiya Talata inda maharan suka bude masu wuta.

An kai harin ne a garin ‘Yar Gamji da ke karamar Hukumar Batsari a jihar ta Katsina.  Wani ganau ya shedawa manema labarai cewa,  lamarin ya faru ne bayan saukar ruwan sama a yankin, inda manoma suka bazama dan yin aiki a gonakinsu kuma ba zato ba tsammani maharan suka bude musu wuta.

Jahar Katsina da ke makwabtaka da jahar Zamfara ta fada cikin yanayi na rashin tsaro a baya-bayan nan bayan da matsalar sace mutane da yin garkuwa da su don neman kudin fansa ya kara yin kamari a sassan kauyukan Zamfaran. DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: