Ko kasashen Turai za su iya shawo kan Iran?

Ko kasashen Turai za su iya shawo kan Iran?

A ranar Lahadi ne manyan jami’an diflomasiyya daga Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China za su gana da takwarorinsu na Iran a birnin Vienna, na kasar Austria, domin duba hanyoyin da za a kare yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015.

Zaman dar-dar ya karu a yankin Tekun Fasha tun bara lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikin shirin, wanda ya rage adadin makamashin nukiliyar da Iran ke ingantawa domin rage mata takunkumin karya tattalin arziki.

Shirin nukiyar na Iran dai na tsaka mai wuya. Amurka ta sake kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki.

Yayin da ita kuma Iran, ta karya ka’idar da aka sanya mata ta adadin makamashin Yureniyam din da za ta inganta.

Kuma ta yi barazanar kara daukar wasu matakan, idan har sauran kasashen da suka sanya hannu a yarjejeniyar – musamman na Turai – ba su dauki matakan da za su rage mata radadin takunkumin da Amurka ta sanya mata ba.

Babbar jami’ar da ke kula da harkokin kasashen waje ta Tarayyar Turai, ta yi kira ga Iran da ta mutunta yarjejeniyar.

Sai dai zaman dar-dar ya karu sakamakon kame wasu jiragen ruwa masu dakon man fetur da kuma harbo wa juna jirage marasa matuka da Amurka da Iran suka yi.

A makon da ya wuce ne Iran ta kama wata tankar dakon mai mai tutar Birtaniya, a wani mataki da ake wa kallon na ramuwar gayya ne kan tankar man Iran da Birtaniya ta kama a yankin Gibraltar.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: