Ko kun san akalla sau nawa ya kamata a motsa jiki a mako?

Ko kun san akalla sau nawa ya kamata a motsa jiki a mako?

Masana harkokin kiwon lafiya sun shawarci mutane da su rika motsa jikinsu sau biyu a mako.

Irin wannan motsa jiki na Tai Chi a kan ja dogon numfashi ne da zai bai wa dukkanin gabban mutum damar karbar sakonnin motsa jikin.

Wannan motsa jikin kan taimaka wa lafiyar bil’adama na dogon lokaci, kamar yadda kwararrun likitoci a Birtaniya suka tabbatar.

A karo na farko, cikin shawarwarin da kwararrun suka bayar akwai batun cewa ya kamata mata masu juna biyu da kuma sabbin haihuwa su mayar da irin wannan motsa jiki al’ada, la’akari da ingancin lafiyarsu.

Daga cikin abubuwan da kwararrun likitocin suka bayar da shawarar ayi su a bangaren, akwai rawa da sunkuyo ko kuma motsa hannaye kama daga kafada zuwa yatsu.

An kuma shawarci ‘yan shekaru 65 zuwa sama da rika yin motsa jiki na Tai Chi domin kauce wa faduwa ba bisa dalili ba saboda tsufa.

Yawan motsa jikin dai na rage kiba, ciwon sikari na type 2 diabetes, ciwon zuciya da kuma yawan bacin rai, a cewar shawarar kwararrun likitocin.

Sabbin matakan motsan jikin da aka yi na’am da su, kwararrun likitoci a Birtaniya sun yi nazari sosai domin yin dai-dai da kimiyyar wannan zamani.

Sakon nasu dai na nuni da cewa maimakon zaman rashin aikin yi, a yi amfani da damar da aka samu wajen motsa jiki domin inganta lafiya.

Wani masanin kiwon lafiya a Ingila, Farfesa Dame Sally Davies cewa ya yi da dama daga cikin kananan yara da kuma manya a Birtaniya ba su son motsa jiki yadda ya kamata.

“Akwai bukatar mu kara yawan tattakin da muke yi. Akwai bukatar mu rika yawan hawa matattakala, maimakon yawan hawa lifta. Akwai bukatar mu kara karfin jikinmu ta hanyar yawan motsawa.”

Daga cikin shawarwarin da likitocin suka bayar sun ce ya kamata tsofaffi su inganta karfin jikinsu ta hanyar motsawa.

Yin hakan yana taimaka musu matuka wajen daidaita tsokar jikinsu da kuma karfin kashi.

Kwararrun likitocin dai sun ce motsa jikin na taimakawa wajen dakile matsalar kashin da mutane ke fama da ita da zarar sun kai shekara 50 da haihuwa.

Ga ‘yan kasa da shekara 5

 • Jarirai – ya kamata a bar su kwance kan ciki na tsawon minti 30 – daga lokacin da jariri ya kwanta a kan cikin a ba shi tsawon wannan lokaci. Sai dai ba ko yaushe ne za su rika yi ba.
 • Yara kanana – mintuna 180 a kowace rana ta hanyar yin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.
 • Yaran da ke gab da shiga makaranta – Ya kamata su dauki tsawon mintuna 180 a kowacce rana suna wasan tsalle-tsalle, kuma ya kamata a ba su minti 60 suna motsawa da karfin jikinsu.

Ga ‘yanshekara 5 zuwa 18

 • Ya kamata su dauki tsawon sa’a guda suna motsa jiki kowacce rana, misali wasannin motsa jiki a makaranta ko doguwar tafiya ko kuma motsa jiki bayan an tashi daga makaranta da kuma sauran wasanni.
 • Motsa tsokar jikinsu da kuma kashi a koda yaushe.
 • Rage yawan zama ko kuma kwanciya.

Ga ‘yan shekara 19 zuwa 64

 • Kasancewa cikin koshin lafiya a kowacce rana.
 • Motsa gabobi ko da yin ban ruwa ne, daukar kaya masu nauyi da kuma yin juriya wajen motsawar ko da sau biyu ne a sati.
 • Yin wasu ayyukan da za su taimaka wajen motsa jikin a kalla har tsawon mintuna 150 , kamar tsere ko yin tattaki ko kuma gudu sau biyu a mako.
 • A kuma rage yawan kwanciya ko kuma zama.

Ga ‘yan sama da shekara 65

 • Yin wasu ayyukan motsa jiki yafi zama haka nan.
 • Yin amfani da kwanaki biyu cikin mako guda wajen inganta lafiyar jiki, irin su rawa ko sunkuyo ko Tai Chi da kuma motsa sauran gabobi.
 • Ya kamata a kowanne mako a yi amfani da mintuna 150 wajen inganta hanyoyin motsa jiki, ta yadda zai bayar da damar kara yawan lokutan da ake amfani da su a baya.
 • Kasancewa mai tsayuwa wajen motsa jiki ko da kadan ne a kowanne lokaci, yin tsayuwa ma kan wadatar da hakan.

Ga mata masu juna biyu

 • Motsa jiki har na tsawon mintuna 150 a kowanne mako.
 • Ba’a son wadanda tun farko basu saba motsa jikin ba, su matsantawa kansu.
 • Kar ayi irin motsa jikin da ka iya shafar yaron da ke ciki.
 • Ya kamata a rika motsa naman jiki da kuma gabobi sau biyu a mako.

Gamata masu sabuwar haihuwa

 • Motsa jiki na tsawon mintuna 150 a kowanne mako.
 • Motsa naman jiki da kuma gabobi sau biyu a mako.
 • Fara motsa jiki na yau da kullum da zaran an samu damar yin hakan.

Ga masu bukata ta musamman

 • Kowanne irin motsa jiki ba illa bane, kuma yana kawo fa’idoji da dama wajen inganta lafiya ga al’ummar duniya.

Wani masanin harkokin motsa jiki daga Birtaniya mai suna Tim Hollingsworth, ya ce yana da kyau a rika motsa jiki a ko yaushe domin inganta lafiyar zuciya.

“Amfanin abin shi ne akwai hanyoyi da yawa da za’a yi amfani da su don inganta karfin jiki, ko da a gida ne, ko wurin motsa jiki ko kuma bayar da gudunmawa a bangaren wasanni.”

“Mayar da hankali sosai wajen yin atisaye, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, domin inganta lafiyar jiki.”

Dakta Max Davie, daga kwalejin nazarin kula da lafiyar yara ta Royal a Birtaniya cewa ya kamata iyaye su bullo da wani shiri na musamman kan harkar motsa jiki a ko yaushe.

Ya ce yawan yin tattaki ko kuma hawa kan keke zuwa wurare kamar makaranta ga misali, shima yana taimakawa wajen inganta lafiya.

“Mun sani cewa yin hakan, yana taimakawa wajen inganta lafiyar kwakwalwa da kuma jiki, ta yadda zai taimaka musu a lokacin girman su.” a cewar sa.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: