Ko Pogba zai yarda a yi musayarsa da Neymar?

Ko Pogba zai yarda a yi musayarsa da Neymar?

Sai Arsenal ta kashe rabin kudaden da ta ware domin sayen ‘yan wasa idan tana son sayen dan wasan baya na Celtic Kieran Tierney mai shekara 22, wanda aka yi wa farashi a kan fan miliyan 25, a cewar jaridar (Telegraph).

Babu tabbas kan makomar dan wasan Croatia Mateo Kovacic a Chelsea, zaman da yake yi daga Real Madrid na aro zai kare daga ranar 1 ga watan Yuli. Kawo yanzu kuma Chelsea ba ta yi masa tayin tsawaita zaman nasa ba, in ji (Goal).

Paris St-Germain ta bai wa Manchester United damar musayar dan wasan Brazil Neymar, da na Faransa Paul Pogba, kamar yadda jaridar (Independent) ta rawaito.

United za su sake yunkurin sayen matashin dan wasan Ingila wanda ke Borussia Dortmund Jadon Sancho, idan suka sayar da Pogba, a cewar jaridar (Sun).

Ba za a bar Neymar ya koma tsohon kulob dinsa na Barcelona daga PSG ba har sai ya nemi gafarar magoya bayan kulob din sannan ya amince a rage masa albashi, a cewar jaridar (El Mundo – in Spanish).

Real Madrid ba za ta saurari duk wani tayi da ya gaza fan miliyan 50 ba kan dan wasan tsakiya na Sifaniya Dani Ceballos, wanda Tottenham ke son saya, in ji jaridar(AS- in Spanish) .

Arsenal na nuna turjiya kan sha’awar da AC Milan ke nunawa kan dan kwallon Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 23, a cewar (Mirror).

Sabon kocin Juventus Maurizio Sarri ya bayyana dan wasan gefe na Tottenham Kieran Trippier, a matsayin dan kwallon da yake so ya fara saya, sai dai Napoli ma na son sa, kuma tuni suka yi magana, in ji Daily (Mirror).

Dan kwallon daArsenal ke nema Dominik Szoboszlai, mai shekara 18, yana matukar son ya koma kulob din Red Bull Salzburg, yayin da Barcelona da Borussia Dortmund suma ke sha’awar dan wasan na kasar Hungary, a cewar shafin (Football.London). BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: