Kotu ta dage sauraron shari’ar Elzakzaky ta neman beli

Kotu ta dage sauraron shari’ar Elzakzaky ta neman beli

Babbar kotun Kaduna da ke sauraron bukatar neman belin shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky da mai dakinsa ta dage sauraron karar har zuwa 5 ga watan Agusta domin yanke hukunci.

A yayin zaman na Litinin dai, lauyan Sheikh Zakzaky, Femi Falana ya shaida wa kotu cewa mutumin da yake karewa yana cikin ‘matsanancin halin rashin lafiyar’ da ke bukatar a fitar da shi kasar waje domin nema masa magani.

Ya kara da cewa a kasar waje ne kawai za a iya duba Sheikh Zakzaky yadda ya kamata saboda ‘tsanantar’ da cutar ta yi.

To sai dai lauyan gwamnati, Debris Bayero ya soki uzurin da Femi Falana ya gabatar a gaban kotun, inda ya ce ba sai an fitar da shugaban IMN din ba kasar waje kasnacewar akwai kwararrun likitocin da za su iya duba shi a cikin gida.

Daga nan ne sai alkalin kotu,Darius Khobo ya dage sauraron karar zuwa biyar ga watan Agusta.

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN dai tana neman a bayar da belin shugaban nata Ibrahim El-zakzaky domin ya fita kasashen ketare a duba lafiyarsa.

An dai kama shi ne tun shekara ta 2015, bisa zargin yunkurin kisan kai da kuma kawo hargitsi, kuma tun lokacin ne magoya bayansa ke zanga-zangar neman a sake shi, lamarin da kan kaisu ga yin mummunar taho-mu-gama da jami’an tsaro.

Shari’ar ta Sheikh Zakzaky na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan da wata kotu a Abuja ta haramta kungiyar tasa da kuma bayyanata a matsayin ta ta’addanci kamar yadda gwamnati ta bukata.

Gwamnati ta ce tayar da hankalin da ‘yay’an kungiyar ke yi ne ya sa ta daukar wannan mataki, batun da suka musanta suna masu cewa kage ake yi musu.

Zaman shari’ar na ranar Litinin wani bangare ne na doguwar shari’ar da aka dade ana yi wa jagoran na Shi’a. Da farko an sa ran cewa za a yanke hukunci kan batun belin nasa a makon da ya wuce, amma kwatsam sai aka dage zaman.

Tun bayan tsare shi a watan Dismbar 2015, magoya bayansa ke ta zanga-zanga domin matsawa gwamnati lamba kan ta sake shi, lamarin da yake kaisu yin taho-mu-gama da jami’an tsaro taro da yin hasarar rayuka da kuma dukiyoyi.

Tarzoma ta baya-bayan nan ita ce wacce ta haifar da mutuwar wani matashin dan jarida na gidan talbijin na Channels da wani babban jami’in ‘yan sanda, da kuma ‘yan Shi’a 11 a makon da ya wuce.

Kungiyoin kare hakkil bi’adama sun yi Allah-wadai da yadda suka ce ‘yan sanda na amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zangar.

A yanzu hankali zai karkata ne kan hukuncin da kotun ta Kaduna za ta yanke kan belin nasa, da kuma martanin da magoya bayansa da kuma gwamnati za su mayar ganin cewa a baya an taba ba shi beli amma aka ki sakinsa.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: