Kun san sana’ar da ke hana ‘yan Nijar cirani?

Kun san sana’ar da ke hana ‘yan Nijar cirani?

Daruruwan matasan sun kafa wani gari da suka yi wa lakabi da Gidan Daka, inda suke aikin nerman zinare ta hanyar fasa duwarwatsu.

Ana dai dauko duwatsun ne daga kasar Algeria da kuma Tchiberkatan wani yanki na jamhuriyar Nijar.

Matasan wadanda suka fito daga sassan kasar daban-daban sun ce sun kafa wannan gari ne dan yaki da zaman banza sakamakon rufe mahakar zinare ta Djado da gwamnatin ta Nijar ta yi.

Ibrahim Abdou na daya daga cikin ma’aikatan hako zinaren inda ya shaida wa BBC yadda suke aikin nasu. Ya ce da “farko suna farawa da fasa duwatsu da hannunsu abin da ake kira marsa-marsa har zuwa matakin karshe na gasa zinaren domin sayarwa.”

Ibrahim ya ce sana’ar na kawo musu kudin da suke bukata domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

To sai dai da dama daga cikin matasan da ke wannan sana’a na fuskantar matsaloli irin na kiyon lafiya saboda kurar da suke shaka

A kan kuma samu yanayin da wasu daga cikin matasan mazauna Gidan Daka kan bi dare suna kwashe abun da wasu suka hako.

Wata ribar wannan sana’a da jamhuriyar Niger ta samu ita ce yadda sana’ar ta hana matasan kasar ketara wa kasashen waje kamar yadda masu sana’ar suka shaida wa BBC cewa ba sa bukatar kama hanya zuwa turai ballantana su mutu a cikin sahara.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: