‘Makashin maza’ zai yi zaman kaso na shekara 30

‘Makashin maza’ zai yi zaman kaso na shekara 30

Kotun hukunta manyan laifukan ta duniya, ICC, ta yanke wa tsohon madugun ‘yan tawayen kasar Congo, Bosco Ntaganda hukuncin zaman gidan kaso na shekara 30, bisa laifukan yaki da cin zarafin mutane.

An dai tuhumi Bosco Ntaganda wanda ake yi wa lakabi “Terminator” ko ‘makashin maza’ da laifuka 18 da suka hada da kisan jama’a da fyade da lalata mata da amfani da kananan yara a aikin soja.

Alkalan kotun ta ICC sun gano cewa a watan Yuli mayaka masu goyon bayan Ntaganda sun aikata kisan kare dangi.

Wannan ne dai karon farko da kotun ta ICC ta yanke hukunci mafi tsayi ga wani.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: