Makomar Arewa

Shirine da gidan Redio kano yake gabatarwa kai tsaye (live) a duk ranar lahadi da daddare, daga karfe 9.00 – 10.00 na dare tare da jami’in shirin. Nuhu Gudaji.
Manufar shirin shine don ya dawo da martabar Aewacin Nigeria. Ta fagen inganta tarbiyya tsakanin dattawa da matasa, ta yanda za’a sami ingantaccen jagoranci da magana da murya daya akan duk al’amuran da suka shafi Arewacin Nigeria musamman abubuwan da suka shafi zamantakewar siyasa, tattalin arziki da matsalolin da suke jawo koma bayan Arewa da hanyoyin da za’a magancesu ta hanyar tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki.misali shaye shayen miyagun kwayoyi da kwararowar Almajirai daga kauyuka zuwa birane.