Mali na zaman makoki na kwanaki 3

Mali na zaman makoki na kwanaki 3

Rikicin kabilanci da ya janyo asarar rayukan mutum sama da talatin ya yi awon gaba da kujerar gwamnan lardin da aka kai kazamin hari a karashen makon da ya gabata a kasar ta Mali.

An sauke Sidy Alassane Toure daga mukamin gwamnan yankin na Mopti ne, bisa hali na sakaci, ganin bai iya gano alamun da suka nuna cewa za a kai wa kauyen na Dongon hari ba balle ma ya nemi daukar mataki. Bayan sanar da korar, Gwamnati ta kuma ayyana kwanaki uku a matsayin ranakun zaman makoki don nuna jimamin rayukan da aka rasa a harin na karshen makon da ya gabata.

Alkaluman farko sun nuna cewa mutum casa’in da biyar ne suka mutu kafin daga bisani a rage adadin zuwa talatin da biyar sai dai mazauna kauyen sun ce rayuka casa’in da biyar din ne suka salwanta. Rikici a tsakani mafarauta da Fulani a Kauyen Dogon ya sha lakume rayuka, inda na watan Maris da mutum dari da hamsin suka mutu a hari na yini guda ya kasance mafi muni a tarihin kasar.

DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: