Man U ta hakura da Maguire, Juventus na neman rance don sayen Pogba

Man U ta hakura da Maguire, Juventus na neman rance don sayen Pogba

Manchester United ta hakura da yunkurin da ta ke yi na sayen dan wasan baya na Leicester Harry Maguire bayan da aka shaida muta cewa dan kwallon zai kai fan miliyan 100, a cewar Daily (Mirror).

Kocin Nice Patrick Vieira, da na Rangers Steven Gerrard da mataimakin kocin Manchester City Mikel Arteta duka na cikin wadanda Newcastleke hasashen dauka domin maye gurbin Rafa Benitez, in ji (Telegraph).

Ana ganin Arteta zai iya maye gurbin Pep Guardiola a Manchester City idan ya bar kungiyar, in ji (Evening Standard).

Shi ma kocinBurnley Sean Dyche yana cikin wadanda Newcastle ke hankoro sai dai za a bukaci su biya fan miliyan 10 a matsayin salala idan har suna son sa, a cewar (Daily Mail).

Wilfred Zaha na son ya koma Arsenal daga Crystal Place sai dai ana ganin dole Gunners su sayar da wasu ‘yan wasan idan har suna son su iya biyan farashin dan kwallon, wanda zai kan fan miliyan 80.

Manchester United za ta gana da wakilin dan wasan Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 24, domin kammala cinikinsa kan fan miliyan 70 daga Sporting Lisbon, a cewar(O Jogo, via Talksport).

Juventus ta nemi kamfanin Adidas da ya tallafa mata da kudi domin ta samu damar sayen dan wasan Manchester United Paul Pogba, in ji (Corriere dello Sport – in Italian).

Manchester City na tattaunawa da Juventus domin sayen dan wasan Portugal mai shekara 25 Joao Cancelo, a cewar jaridar (Tuttomercato, via Star).

Dan wasanArsenal da Uruguay Lucas Torreiras yace AC Milan ba ta tuntube shi ba da nufin shawo kansa ya koma Italiya da murza leda, in ji (Talksport).

Bayern Munich ta tattauna da wakilin dan wasan Barcelona da Faransa Ousmane Dembele a yunkurinsu na sayen dan kwallon mai shekara 22, in ji Daily (Mirror).

Dan wasan baya na Netherlands mai shekara 17 Sepp van den Berg, na dab da komawa Liverpool daga PEC Zwolle, a cewar(Evening Standard).

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: