Mutum 700 aka sace a Najeriya daga farkon 2019 zuwa yanzu – Masana tsaro

Mutum 700 aka sace a Najeriya daga farkon 2019 zuwa yanzu – Masana tsaro

Masu sharhi a Najeriya sun ce halin tabarbarewar tsaro na kara sanya fargaba a zukatan ‘yan kasar, duk da cewa hukumomi suna cewa matsalar ba ta kai yadda ake zuzutawa ba.

Ko a yammacin ranar Lahadi ‘yan sanda sun ce sun kubutar da wani babban jami’insu daga hannun masu satar mutane don neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Jos.

Malam Kabiru Adamu wani kwararre ne kan harkokin tsaro a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa daga watan Janairun 2019 zuwa yanzu an sace mutum 700 a fadin kasar.

“Bisa ga alkaluman da muke da su, a bana kawai an sace dan adam dai-dai har misalin 700 a fadin kasar. Wadannan alkaluma ba wai dole ba ne abin ya zama haka yake amma gwaji ne wanda zai nuna wa duk mai bibiyar lamarin inda matsalar take,” in ji shi.

Masanin tsaron ya kara da cewa alkaluman sun nuna jihar Ribas ce wannan matsala ta satar mutane ta fi kamari, daga can sai Kaduna da Zamfara da kuma Katsina.

Ya ce: “Matsalar jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara shi ne ba kasafai suke iya kai wa hukuma rahoto ba don haka samun cikakkun alkaluman yadda za a bi a kimiyance yana da wahala.

“Wannan 700 din ma da na fadi mun yi amanna yawan ya fi haka amma dai yana ba mu dama mu fahimci yadda matsalar take da kuma yadda ake sace-sacen.”

Malam Kabiru ya ce Najeriya ta fara zama kasashe irinsu Mexico inda matsalar tsaro ta tabarbare, “kuma hakan yana matukar shafar walwalar ‘yan kasa da ma baki”, a cewarsa. An shafe tsawon lokaci Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban da suka hada da satar mutane don kudin fansa.

Ko babban birnin tarayyar kasar ma Abuja bai tsira ba inda a baya-bayan nan ake samun rahotanni sace mutane a unguwannin da ke wajen gari wasu lokutan ma har a cikin garin.

A jihohi irin su Kano kuma satar kananan yara ce ta addabi mazauna birnin Kano din.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: